WAKILAN GIDAUNIYAR MMAWT LEGACY INITIATIVE SUN HALARCI TATTAUNAWAR DA KUNGIYOYIN MATA SUKAYI DA SHUGABAN DANDALIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA 74, FARFESA TIJJANI MUHAMMAD BANDE

WAKILAN GIDAUNIYAR MMAWT LEGACY INITIATIVE SUN HALARCI TATTAUNAWAR DA KUNGIYOYIN MATA SUKAYI DA SHUGABAN DANDALIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA 74, FARFESA TIJJANI MUHAMMAD BANDE
November 26, 2019 mmawt

Taron wanda minister mata, Dame Pauline Tallen ta shirya ya samu halartar kungiyoyin mata daga sassa daban daban, da kuma manyan wakilan gwamnati da suka hada da Dakta Hajo Sani, babbar mai baiwa matar shugaban kasa shawara, matar Gwamnan jihar Ekiti, Bisi Fayemi, ministar agajin gaggawa, Hajiya Sadiya Umar Faruk, tsohuwar ministar mata, Josephine Anenih da wakiliyar bangaren mata ta majalisar dinkin duniya, comfort Laptey.

A jawabin ta, Dame Pauline Tallen, ta godewa Farfesa Bande kan halartar taron tare da yin bayanai kan abubuwan dake dakile cigaban mata, tare da neman tallafi domin ganin cewa mata sun more da shirye shirye muradun karni.

Itama matar Gwamnan jihar Ekiti tayi kira da a tsaurara dokoki domin hana cin zarafin mata da kananan yara. Itama wakiliyar majalisar dinkin duniya ta tofa albarkacin bakinta tare da alkawarin kara kokari domin kawo cigaba a harkokin mata.

Da yake maida martani, farfesa Bande ya nuna jin dadin sa da ganin yadda mata suka maida himma domin ganin cewa an dama dasu ta bangarori daban daban, tare da alkawarin bada goyon baya ga duk shiraruwan da zasu kyautata rayuwar mata da yara.

An kuma shawarci uwaye da su koyawa yaya maza muhimmancin girmama da mutunta yaya mata, bude wuri na musamman domin kula da matan da aka ci zarafin su da sauran su. An kuma kunna kyandur domin tunawa da mata wadanda suka rasa rayukan su a dalilin tsangwama ko fyade da makamantan su.

0 Comments

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*